Somaliya : Dakarun AU Sun Hallaka Yan Al-Shabaab Sama da 100
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6526-somaliya_dakarun_au_sun_hallaka_yan_al_shabaab_sama_da_100
Sojojin kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) dake Somaliya sun bayyana cewa, dakarun AMISOM da na gwamnatin Somaliya sun yi nasarar hallaka 'yan kungiyar Al-Shabaab sama da dari a tsakiyar kasar.
(last modified 2018-08-22T11:28:25+00:00 )
Jun 10, 2016 11:19 UTC
  • Somaliya : Dakarun AU Sun Hallaka Yan Al-Shabaab Sama da 100

Sojojin kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) dake Somaliya sun bayyana cewa, dakarun AMISOM da na gwamnatin Somaliya sun yi nasarar hallaka 'yan kungiyar Al-Shabaab sama da dari a tsakiyar kasar.

kakakin kungiyar Al-Shabaab ya bayyana cewa, 'yan kungiyar sun kai harin kunar bakin wake da bama-bamai kan wani barikin rundunar sojojin kungiyar AU dake yankin tsakiyar Habasha, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin kiyaye zaman lafiya na Habasha kimanin 60.

Sai dai har yanzu tawagar AU din ba ta tabbatar da gaskiyar lamarin ba.

Mayakan Al'shabab dai sun jima suna amfani da irin wannan salo wajen kai hariwa dakarun sulhu na tarraya Afirka, inda ko a watan janairun daya gabata, wani hari makamacin wannan yayi sanadin mutuwar sojojin Kenya sama da 100.