Sudan Ta Kudu : Salva Kiir Ya Nada Riek Machar Mataimakin Sa
Feb 12, 2016 05:35 UTC
-
shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riak Mashar
Wannan matakin dai na cikin yerjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma a watan Agusta 2015 a shiga tsakanin MDD
Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kir a safiyar yau juma'a ya sake nada shugaban yan tawayen kasar Riek Machar mataimakinsa.
Wannan matakin dai na cikin yerjejeniyar da bangarorin biyu suka cimma a watan Agusta a shiga tsakanin MDD domin kawo karshen yakin basasa daya daidaita jinjira kasar.
Mr. Machar dai dama ya taba zama mataimakin shugaba Kiir a tsakanin shekarun 2005-2011 a lokacin Sudan ta kudu bata samu incin kan ta ba daga Sudan, kafin daga bisani shugaba Kiir ya tsige shi daga mukamin mataimakin sa a watan Yuli 2013.
Tags