Gwamnatin Nigeria Ta Jaddada Bukatar Tattaunawa Da Tsageran Niger Delta
Wata majiyar sojojin a tarayyar Nigeria ta bada sanarwan cewa har yanzun gwamnatin kasar tana bukatan kawo karshen rikicin da ke faruwa a yankin Niger dalter ta hanyar tattaunawa.
Wata majiyar sojojin a tarayyar Nigeria ta bada sanarwan cewa har yanzun gwamnatin kasar tana bukatan kawo karshen rikicin da ke faruwa a yankin Niger dalter ta hanyar tattaunawa.
Kamfanin dillancin Labarai Chinhuwa na kasar China ya nakalto wani babban jami'in sojojin kasar wanda baya son a bayyana sunansa yana cewa a jiya jumma'a ma wasu boma boman sun tashi sun kuma lalata wasu bututan mai a yankin. Fasa bututan mai a yankin na Niger Delta dai ya ya rage yawan man da kasar take fitarwa zuwa kasuwannin duniya, sanadiyyar hakan kuma ya jawo tashin farashin man a kasuwannin na duniya .
Wata kungiya mai suna "Niger delta Avengers" ce take daukar nauyin fasa bututam mai a yankin tun makokki da suka gabata.