Rwanda Na Son Maida 'Yan Gudun Hijira Burundi Wasu Kasashe
-
shugaba Paul Kagame na Ruwanda
Wannan matakin ya biyo bayan zargin da ake ma mahukuntan kasar na taimakawa 'yan tawayen dake son kifar da gwamnatin Burundi
Hukumomi a kasar Ruwanda na shirin maida 'yan gudun hijira Burundi dake zaune a kasar zuwa wasu kasashe.
Wannan matakin ya biyo bayan zargin da aka jima ana ma mahukuntan Ruwanda na tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na Burundi.
Gwamnatin Ruwanda ta sanar a yau cewa zata shiga aikin tare da abokan hulda na kasashen duniya domin shirya maida 'yan gudun hijira wasu kasashe cikin tsari, tare da mutunta 'yan gudun hijira
A makon daya gabata wasu kwararu daga MDD sun zargi Ruwanda da horada 'yan gudun hijira Burundi domin kifar da gwamnatin shugaba Pierre Nkurinziza, zargin da mahukuntan Ruwanda suka jima suna musuntawa.