Yajin Aikin Masu Burodi A Kasar Borkina Faso:
Jun 11, 2016 18:51 UTC
Ma'aiaktan Gidan Burodi Sun Tsunduma Yajin Aiki Saboda Karancin Albashi.
Shugaban kungiyar ma'aikatan gidan burudon Konomba Traore ya sanar da cewa saboda wadanda su ka mallaki gidajen burodin sun ki amincewa da kara wa ma'aikatansu albashi da kaso 25%, sun tsunduma yajin aiki.
Tun daga ranar alhamis din da ta gabata ne dai aka rufe mafi yawancin gidajen burodin da ke kasar kuma har zuwa yau asabar ba a bude su ba.
Ministan ciniki na kasar ta Burkina Faso, Stephane Sanou ya sanar da cewa sun bude tattaunawa da kungiyoyin ma'aiakatan domin kawo karshen yajin aikin.
Burodi dai yana da matukar muhimmancin a rayuwar yau da kullum ta mutanen kasar Burkina Faso.
Tags