An Hallaka Mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Nigeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6601-an_hallaka_mayakan_boko_haram_a_arewa_maso_gabashin_nigeriya
Dakarun tsaron Najeriya sun sanar da hallaka mayakan boko haram a shiyar Arewa maso gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 12, 2016 01:09 UTC
  • An Hallaka Mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Nigeriya

Dakarun tsaron Najeriya sun sanar da hallaka mayakan boko haram a shiyar Arewa maso gabashin kasar

A cikin wata sanarwa da ta fitar Jiyar Assabar, Rundunar sojin Najeriya ta ce a ci gaba da tsarkaka yankunan kasar daga mamayar kungiyar Boko haram sun hallaka mayakan boko haram 10 a garin Gamboru-Ngala dake jihar Borno a shiyar Arewa maso gabashin kasar.

Sanarwa ta ce bayan mayakan bokon da aka hallaka, Sojoji sun samu nasarar kame guda biyu da ransu.

Har ila yau rahoton ya ce Dakarun tsaron Najeriyan, sun gano makamai kungiyar boko Haram din da wasu ababen fashewa a wannan farmaki.

Tun a shekarar 2009, kungiyar boko haram din ta fara kai hare-haren ta'addanci a Najeriya, inda daga baya ta fadada kai hare-haren ta a kasashen dake makobtaka da kasar kamar su Tchadi, Kamaru da Niger, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane kimanin dubu dari biyu yayin da wasu sama da million 2 da dubu 600 suka yi gudun hijra.