Mayakan Boko Haram Sun Kashe mutane 4 A Jiya Asabar Da Yamma
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6619-mayakan_boko_haram_sun_kashe_mutane_4_a_jiya_asabar_da_yamma
Mayakan kungiyar yan ta'adda ta boko haram sun kashe mutane 4 a wani kauye kusa da birnin Maiduguri
(last modified 2018-08-22T06:58:26+00:00 )
Jun 12, 2016 07:21 UTC
  • Mayakan Boko Haram Sun Kashe mutane 4 A Jiya Asabar Da Yamma

Mayakan kungiyar yan ta'adda ta boko haram sun kashe mutane 4 a wani kauye kusa da birnin Maiduguri

Mayakan kungiyar yan ta'adda ta boko haram sun kashe mutane 4 a wani kauye kusa da birnin Maiduguri babban birnin Jihar Borno a Arewa maso gabacin tarayyar Nigeria.

Kamfanin dillancin labarai na Rasha Today ya ce a jiya da dare ne mayakan na Boko haran suka kai hari kan wani kayu kusa da birnin Maiduguri inda suka yanke mata gudu 4, wadanda suke tsakanin shekaru 28-48. Laifin wadan nan mata wa Boko haram shi ne mazajensu ko sunki aiki tare da Boko haram ko kuma suna zarginsu da tallafawa gwamnatin kasar a kansu.

Kungiyar Boko Haram dai ta fara fafatawa da jami'an tsaron Nigeria ne tun shekara 2009 kuma ya zuwa yanzu dubban mutane ne suka kashe a yankin Arewa maso gabancin Nigeria sun kuma tilastwa miliyoyi kauracewa gidajensu.