Da Alamun Gwamnatin Tarayyar Nigeria Ta Fara Sasantawa Sa Tsagerun Niger Delta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6667-da_alamun_gwamnatin_tarayyar_nigeria_ta_fara_sasantawa_sa_tsagerun_niger_delta
Da alamun gwamnatin Nigeria ta sami damar haduwa da tsagerun Niger Delta ta NDA daga bayan fage
(last modified 2018-08-22T06:58:26+00:00 )
Jun 13, 2016 06:49 UTC
  • Da Alamun Gwamnatin Tarayyar Nigeria Ta Fara Sasantawa Sa Tsagerun Niger Delta

Da alamun gwamnatin Nigeria ta sami damar haduwa da tsagerun Niger Delta ta NDA daga bayan fage

A alamun gwamnatin tarayyar Nigeria ta sami haduwa da shuwagabannin kungiyar tsagerun Niger Delta NDA don fara tattaunawa kan dawo da zaman lafiya a yankin. Gwamnatin tarayyar Nigeria ta kasa fitar da ganga 800,000 na danyen man fetur a yankin a ko wace rana sanadiyyar fasa bututan man wanda kungiyar NDA suka yi ta yi. Hakan dai ya jawo asara mai yawa ga gwamnati.

Majiyar jaridar This Day ta Nigeria ta bayyana cewa gwamnatin Nigeria karkashin mataimakin shugaban kasa Prof. Osinbajo ta kafa komitin don warware matsalar yankin. Membobin komitin sun hada da Maj. Gen. Babagana Monguno, mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro da kuma Ministan man fetur Ibe Kachikwu.

Da alamun komitin ya sami damar haduwa da shuwagabannin kungiyar ta NDA ta bayan fage, don an ga tsaigata fasa bututan a cikin kwanakin da suka gabata.

Kafin haka dai Prof. Osinbajo ya gana da gwanonin yankin don tattauna yadda zasu bullowa lamarin.