An Dauki Tsauraran Matakan Tsaro A Gabashin Kenya
An dauki tsauraran matakan tsaro a yankunan Mombasa da ke gabashin kasar Kenya, bisa zaton da ke y na cewa kungiyar Al-shabab na shirin kaddamar da hare-hare a wannan yanki a cikin wannan wata na azumin ramadan.
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa ya bayar da rahoton cewa, Gwamnan Mombasa Mu'allim uhammad ya sheda cewa, al'ummomin yankin wadanda akasarinsu musulmi ne, suna baiwa jami'an tsaro hadin gwaiwa, domin fuskantar barazanar ad suke fuskanta daga 'yan ta'adda.
Jaridar Digital Standard ta yanar gizo ta bayar da rahoto a shafinta cewa, jami'an tsaron kasar Kenya sun samu wasu bayanai ne ta hanyar yanar gizo, dangane da shirin da 'yan ta'addan suke da shi na kadamar da farmaki kan musulmin yankin Mumbasa alokacin azumi.