Damuwar MDD Kan Halin Da 'Yan Gudun Hijira Boko Haram Ke Ciki
MDD ta nuna cewa halin da 'yan gudun hijira na Boko haram ke ciki abun damuwa ne matuka, duba da yadda 'yan gudun hijira ke bukatar taimakon gaggawa.
Alkaluman da MDD ta fiyar sun nuna cewa mutane dubu 40 ne da rikicin Boko Haram na baya-bayan nan ya raba su da gidajensu ke zaune a garin Bosso dake kan iyakokin kasashen Najeriya da Nijer.
Ofishin MDD mai kula da ayyukan jin kai ya tabbatar da cewar, akwai rashin kyawan yanayin tsaro a yankin na Bosso a sakamakon kazamin harin da tsagerun Boko haram suka kai a yankin, kamar yadda mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric ya tabbatarwa da manema labarai hakan.
Tun a ranar 7 ga watan Yuni, hukumomi da kungiyoyin ba da agaji suke ci gaba da yin nazari game da irin kayayyakin tallafin da ake bukata a yankin da nufin shigar da kayan tallafi zuwa yankunan.
Mai magana da yawun MDD ya ce, ya zuwa yanzu, hukumomin agajin sun samu nasarar shigar da tallafin ruwan sha da biskit da motar daukar marasa lafiya.
Sai dai kawo yanzu kashi 25 ne kadai aka samu na kudaden da ake bukata don gudanar da aikin jin kai a yankin Diffa daga cikin dala miliyan 74 da ake bukata, kuma tuni aka fara amfani da kudaden domin samar da kayayyakin da ake da matukar bukatarsu.
A Jamhuriya Kamaru ma MDD tayi hasashe irin wannan inta ta bayyana cewa hare-haren boko haram a kasar sun jefa dubban mutane cikin matsalar rashin abinci, wanda kuma a cewar ta babban abin damuwa ne.
kimanin mutane 190.000 yanzu haka ke cikin hali kaka-ni-kayi a cewar babbar jami'ar kula da harkokin jin kai na MDD reshen Afrika, Najat Rochdi.
Jami'ar ta ce akwai bayanai dake nuna cewa 'yan boko haram sannu a hankali na kai hare-hare tare da kona kauyuka da gidaje da gonaki lokaci zuwa lokaci, wanda a cewar ta ke nuna cewa har yanzu fa ba'a gama murkushe kungiyar ba.
Ta ce lalle hare-harem jifa-jifa ne aman fa sannu a hankali suna daukan hankali.
kawo yanzu dai a cewar MDD yawan mutanen da matsalar rashin abinci ta shafa daga watan Janairu na wannan shekara ya haura daga dubu tara (900,000) zuwa Miliyam biyu da dari hudu (2,400,000).
Abun babban damuwa kuma a cewar Najat Rochdi, shi ne har yanzu ba'a kai ga hada kudaden da ake bukata ba don agazawa wadanda matsalar ta shafa, inda kawo yanzu kashi 30% ne kawai na kudade $ Miliyan 280 da ake bukata aka samu.
A halin da ake ciki dai kasashen Najeriya da kamaru sun cimma yarjejeniya guda hadin gwiwa da MDD kan maido da ‘yan gudun hijirar Boko Haram dubu 80 da ke zaune a Kamaru.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ce ta sanar da haka bayan samun jituwa tsakanin Najeriya da Kamaru.
Kakakin hukumar agajin gaggawa NEMA a Najeriya Sani Datti, ya ce za 'a dawo da ‘Yan Najeriya ne da suke son su dawo kasarsu.
A can baya dai Kamaru ta taso keyar wasu dubban ‘Yan Najeriya ba da son ransu ba, akan haka ne kuma kasashen biyu suka cimma yarjejeniyar dawo da wadanda ke ra’ayin dawo wa.
Alkalumen MDD sun nuna cewa 'yan gudun hijira dubu dari biyar (500,000) ne rikicin boko haram ya raba da gidajen su saboda rikicin na boko haram a yankin arewa mai nisa na kasar ta kamaru.
Kuma bisa la'akari da yadda damuna ta danno kai ya kamata a dauki matakan gaggawa na samarwa da 'yan gudun hijira matsugunai masu karko, da abunci da kuma kayayakin bukata na yau da kulun dama fadakar dasu hanyoyin kiyaye sabta.
hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta ce a yanzu dai kwararen 'yan gudun hijira ya rage matuka a Kamaru, aman abun damuwa shi ne 'yan gudun hijira dake girke