'Yan Adawa sun baiwa Gwamnatin Kenya wa'adin sa'o'i 48
'Yan Adawa a kasar Kenya sun baiwa Gwamnati wa'adin sa'o'i 48 da ta gudanar da gyara a kwamitin gudanar da zabe a kasar
Mista Johnston gungu a gamyar jami'uyn adawa masu neman canji da tabbatar da Democradiya a kasar Kenya ya tabbatar da cewa matukar Gwamnati ba ta gudanar da canji a kwamitin dake gudanar zabe a kasar ba, za su tsananta zanga-zangar a fadin kasar gaba daya.
Mista Johnston ya ce kungiyoyin siyasar kasar Kenya na bukatar warware matsalar siyasar kasar ne ta hanyar tattaunawa, amma har yanzu Gwamnati ta yi burus da bukatar 'yan adawar na kawo gyara a kwamitin zaben kasar.
Gamayar kungiyoyin 'yan adawar sun zarki Gwamnati da baiwa magoya bayanta manyan mukamai a kwamitin dake gudanar da zaben kasar domin haka suka ce babu yadda za ayi a tabbatar da adalci a zaben, lamarin da ya sanya Gamayar Jam'iyun 'yan adawar suka fara gudanar da zanga-zanga , inda kuma suke cin karo da fishin 'yan sanda.
Ya zuwa yanzu borin siyasar ya lashe rayukan Mutane biyu yayin da ya jikkata wasu da dama na daban a kasar ta kenya.