MDD: Fararen Hula Dubu 80 Ne Suka Kaurace Ma Yankunansu A Darfur
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6742-mdd_fararen_hula_dubu_80_ne_suka_kaurace_ma_yankunansu_a_darfur
Bababn jami'in jami'in majalisar dinkin duniya mai sanya idanu kan ayyukan wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin majalisar da kuma kungiyar tarayyar Afirka a yankin Darfur da ke yammacin Sudan ya bayyana cewa, dubban mutane sun tsere daga gidajensu sakamakon tashe-tashen hankulan baya-bayan nan a Darfur.
(last modified 2018-08-22T06:58:26+00:00 )
Jun 15, 2016 01:21 UTC
  • MDD: Fararen Hula Dubu 80 Ne Suka Kaurace Ma Yankunansu A Darfur

Bababn jami'in jami'in majalisar dinkin duniya mai sanya idanu kan ayyukan wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa tsakanin majalisar da kuma kungiyar tarayyar Afirka a yankin Darfur da ke yammacin Sudan ya bayyana cewa, dubban mutane sun tsere daga gidajensu sakamakon tashe-tashen hankulan baya-bayan nan a Darfur.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin rahoton da Ladso ya mika wa majalisar dinkin duniya, ya bayyana cewa daga tsakiyar watan Janairun farkon wannan shekara ya zuwa wannan wata na Yuni, kimanin mutane dubu 80 ne suka bar yankunansu a Darfur.

Ya ce hakan sakamako ne na ci gaba da kai ruwa rana da ake yi tsakanin 'yan tawaye masu biyayya ga Abdulwahid Nur da kuma dakarun gwamnati a yankin Jabal Murrah, ya ce kafin lokacin akwai wasu mutane kimanin dubu 60 da aka tsugunnarsu, inda a halin yanzu adadinsu ya kai dubu 127 a cikin sansanon 60 na majalisar dinkin duniya da ke yankin.