DSS: Muna Tsare Da ZakZaky Ne Don Tsaron Lafiyarsa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6754-dss_muna_tsare_da_zakzaky_ne_don_tsaron_lafiyarsa
Hukumar yansandan ciki (DSS) a Nigeria ta ce tana tsare da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ne saboda tsaron lafiyan.
(last modified 2018-08-22T06:58:27+00:00 )
Jun 15, 2016 06:41 UTC
  • DSS: Muna Tsare Da ZakZaky Ne Don Tsaron Lafiyarsa

Hukumar yansandan ciki (DSS) a Nigeria ta ce tana tsare da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ne saboda tsaron lafiyan.

Hukumar yansandan ciki (DSS) a Nigeria ta ce tana tsare da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ne saboda tsaron lafiyan. Hukumar ta bayyana haka ne a lokacinda take kare kanta kan karar da shugaban harka Islamia a Nigeria ya shigar a gaban wata kotu a Abuja inda yake neman a DSS ta sake shi a kuma biya shi diyya na Naira billion 2.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta nakalto Tijjani Gazali lawyan da ke wakiltan DSS yana fadar haka a jiya, ya kuma kara da cewa hukumar ba zata saki Elzakzaky ba don mutanen unguwar gellesu a Zaria na jihar Kaduna suna da matsala da shi.

Amma Festus Okoye na masu shigar da kara, wanda kuma yake wakiltan Femi Falana (SAN) ya ce abinda hukumar DSS ta fada yana da rikitarwa don Zakzaky bai da wani abu a unguwar Gellesu a halin yanzu, sanadiyar rusa su da sojoji da kuma gwamnatin kaduna suka yi. Don haka injishi Zakzaky bai da warin zuwa A Zaria.

Alkalin babban kotun tarayyar Justice Gabriel Kolawole ya dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan yuli mai kamawa.