An Kashe Masu Dauke Da Makamai A gabacin Kasar Congo
Sojojin Demokradiyyar Congo Sun Kashe Masu Dauke Da Makamai A Gabacin Kasar.
An kashe mutane biyu masu dauke da makamai a gabacin kasar Demokradiyyar Congo.
Radiyon Okapi na kasar Demokradiyyar Congo ya Ambato mai makaga da yawun sojojin kasar Guillaume Ndjike yana cewa; A cikin kwanaki biyu na bayan nana da sojojin kasar su ka kai farmaki sun kasha yna kungiyar nan da ake kira; Mai-mai masu dauke da makamai, yayin da kuma su ka kama wasu biyu.
Kakakin Sojan na Demokradiyyar Congo ya ci gaba da cewa; Sun kuma samu wasu makamai a tare da mutanen da su ka kashe.
Shekaru masu yawa a baya kenan dai da gwamnatin kasar ta ke neman shugaban kungiyar Mai-mai mai suna Tabo Taberi alias ruwa a jallo. Ana tuhumar Taberi dai da aikata laifuka akan bil'adama.
Yankin gabacin kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo yana cike da kungiyoyin 'yan tawaye na cikin gida da kuma kasashen makwabta da su ke dauke da makamai.