Fari Yana Barazana Ga Al'ummar Kasar Madagascar
Karancin abinci yana barazana ga rayukan mutane kimanin miliyan biyu da suke rayuwa a yankunan karkara da suke kasar Madagascar.
Rahotonni suna bayyana cewa; Karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki suna barazana ga mutane kimanin miliyan guda da suke rayuwa a kauyukan da suke kudancin kasar Madagascar, inda a halin yanzu haka jama'a musamman kananan yara suke farautar kananan dabbobi da kwari a matsayin maganin yunwa.
Wani jami'in Hukumar kula da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Madagascar ya bayyana cewa; Matsalar karancin abinci a yankunan kudancin kasar ta Madagascar tana tsananin barazana ga al'ummar yankunan da yawansu suka kai kimanin miliyan biyu lamarin da ke bukatar hanzarta daukan matakan shawo kan matsalar.