Sudan Na Karbar 'Yan Gudun Hijira Sudan Ta Kudu 230.000
Offishin kula da ayyukan jij kai na MDD ya sanar da cewa yawan 'yan gudun hijira Sudan ta kudu dake rayuwa a nakofciyar kasar Sudan ya kai 232.000 tun dai bayan yakin basasar daya daidaita kasar.
Sudan ta kudu dai ta samu incin kan ta ne daga Sudan a cikin shekara 2011 kafin daga bisani ta fada cikin yakin basasa da yayi sanadin mutuwar dubban fararen hula.
Alkalumen da MDD ta fitar sun nuna cewa Sudan na karbar 'yan gudun hijira Sudan ta Kudu mafi yawa.
ko baya ga wannan adadin akwai 'yan gudun hijira Sudan ta Kudun 230.000 dake rayuwa a kasar Habasha, sai kuma wasu 202.000 a Uganda, sanan kuma akwai wasu 57.000 a Kenya.
Hukumar OCHA data fitar wannan rahoto ta nuna mayukar damuwar ta dangane halin da 'yan gudun hijira ke ciki, kuma babban abun damuwa a cewar ta shi ne yadda kashi 13% ne kawai na kudaden da ake bukata don taimaka masu cikin $ Milyan 141 aka samu.