Buhari Ya Jinkirta Komawarsa Gida
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinkirta komawarsa gida daga Landon, inda yake jinya, kamar yadda mataimakin shugaban Yemi Osinbajo ya sanar.
A wannan Alhamis ya kamata Buhari ya koma Najeriya, saidai a cewar Mr Osinbajo Buhari sai ranar Lahadi Buhari zai koma gida.
Buhari dan shekaru 73, ya bar Najeriya ne ranar 6 ga wata saboda ciwan kunne dake damunsa, lamarin daya sa ya ziyarci likitoci a London domin duba lafiyarsa a domin yin riga kafi a cewar fadar shugaban kasar.
M. Osinbajo, ya ce shugaban na cikin koshin lafiya kuma zai iya komawa bakin aikin sa ranar Litinin, tare da jaddada babu wata damuwa dangane da rashin lafiyarsa.
Shugaba Buhari dai ya katse wasu mahimman ziyarce- ziyarce har uku kafin ya je London, wadanda suka hada da Lagos cibiyar kasuwancin kasar, da yankin Niger Delta mai arzikin man fetur dake fuskantar hare-haren tsageru, da kuma taron koli na kungiyar ECOWAS.
Batun rashin lafiyar Buhari dai ya tayar haifar kace-nace ba kadan ba tsakanin al'umma a Najeriya, sanan fadar shugaban kasar bata fiye bada cikakun bayanai ba akan rashin lafiyar shugaban, lamarin dake damun 'yan kasar a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar tabarbarewar tattalin arziki.