Nijar: An kai hari akan sansannin 'yan gudun hijira:
Jun 17, 2016 01:22 UTC
Muhammad Bazoum: An kai yan gudun hijira hari:
Jaridar Lo Figaro ta Faransa ta ambato ministan harkokin cikin gidan Jamhuriyar Nijar, Muhammad Bazoum yana cewa; A jiya alhamis an kai hari akan sansanin 'yan gudun hijira da ke Nguagam mai nisan kilo mita 40 daga Difa.
Ministan harkokin cikin gidan na Nijar ta kuma ci gaba da cewa; An kai harin ne jim kadan bayan ziyarar da wata tawagar gwamnati ta kai a sansanin.
Shi dai sansanin 'yan gudun hijira na Nguagam, yana dauke da wadanda rikicin bokoharam ya koro ne daga gidajensu.
Ministan harkokin cikin gidan kasar ta Nijar ya ci ga cewa; Har kawo ya zuwa yanzu dai babu wasu cikakkun bayani akan harin.
Tags