Benin Ta Rufe Ofisoshin Jakadanci 9
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6853-benin_ta_rufe_ofisoshin_jakadanci_9
Kasar Benin TA Rufe Ofisoshin Jakadancinta 9 a Kasashe daban-daban na duniya
(last modified 2018-08-22T06:58:27+00:00 )
Jun 17, 2016 01:59 UTC
  • Benin Ta Rufe Ofisoshin Jakadanci 9

Kasar Benin TA Rufe Ofisoshin Jakadancinta 9 a Kasashe daban-daban na duniya

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua daga birnin Kotoko babban birnin kasar ta Benin, ya ambato ofishin shugaban kasar yana cewa;

Za a fure ofisoshin jakadanci biyar a cikin nahiyar Afirka, sai kuma guda a gabas ta tsakiya, sai wasu guda biyu a nahiyar Afirka.

Shugaban Ofishin Shugaban Kasar ta Benin Pascal Koupaki ya yi karin bayani da cewa ofisoshin jakadancin kasar da za a rufe a nahiyar Afirka sun hada Cote De Voire da Gabon da Congo, amma za a maida su zama kananan ofisoshin jakadanci.

Koupaki ya ci gaba da cewa; Daya daga cikin dalilan daukar wannan matakin shi ne rage kudaden da ta kasar ta kashe kashewa a harkar diplomasiyya.

Wasu matakan da kasar ta dauka sun kunshi rufe jami'an diplomasiyya masu wakiltar soja, da kuma rage yawan ma'aikatan.