Rikicin Shugabanci A Jam'iyyar PDP Na Ci Gaba Da Munanan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6892-rikicin_shugabanci_a_jam'iyyar_pdp_na_ci_gaba_da_munanan
Rahotanni daga Nijeriya na nuni da cewa rikicin shugabanci a Jam'iyyar PDP, babbar jam'iyyar adawa a kasar, ya ci gaba da kamari sakamakon ci gaba da zafafafn kalamai da kuma barazanar da magoya bayan bangarorin da suke rikicin suke wa junansu.
(last modified 2018-08-22T06:58:27+00:00 )
Jun 18, 2016 06:26 UTC
  • Rikicin Shugabanci A Jam'iyyar PDP Na Ci Gaba Da Munanan

Rahotanni daga Nijeriya na nuni da cewa rikicin shugabanci a Jam'iyyar PDP, babbar jam'iyyar adawa a kasar, ya ci gaba da kamari sakamakon ci gaba da zafafafn kalamai da kuma barazanar da magoya bayan bangarorin da suke rikicin suke wa junansu.

Rahotanni sun ce magoya bayan Sanata Ali Modu Sheriff, daya daga cikin mutanen da ake fafatawa da su dangane da shugabancin jam'iyyar, sun mamaye helkwatar jam'iyyar da ke Abuja dauke da muggan makamai suna masu cewa ba za su bar wani ya shiga helkwatar ba in ba Sanata Sherif din ba wanda a kwanakin baya wasu manyan jam'iyyar suka sanar da sauke shi a matsayin shugaban jam'iyyar da kuma nada Sanata Ahmad Makarfi a matsayin sabon shugaban jam'iyyar.

Hakan kuwa yana zuwa ne bayan kokarin da jami'an tsaron kasar suke yi na shanyo kan rikicin don kada ya ba zu da zama babbar barazana ga tsaro da zaman lafiya kasar.

Rahotannin sun ce babban sufeto janar na 'yan sandan Nijeriyar, Solomon Arase, ya gana da bangaren Sanata Ali Modu Sheriff da kuma Sanata Ahmed Makarfi a ofishinsa da ke Abuja don samar da hanyar da za a bi wajen sasanta rikicin. A saboda haka ne ma ya sanar da cewa helkwatar jam'iyyar da ke Wadata Plaza a Abuja za ta ji gaba da zama a rufe har sai an magance rikicin.

Rikicin PDP din ya faro ne bayan da wani taro da dattawan jam'iyyar suka gudanar ne inda suka nada Sanata Ahmad Makarfi a matsayin shugaban jam'iyyar da kuma sauke Sanata Ali Modu Sheriff, wanda ke shugabancin rikon-kwarya na jam'iyyar.