An gano gawawwakin 'yan gudun hijrar Habasha 19 a D/Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6907-an_gano_gawawwakin_'yan_gudun_hijrar_habasha_19_a_d_congo
Magabatan Ma'aikatar 'yan gudun hijra ta kasar D/Congo ta sanar da gano gawawwakin 'yan gudun hijrar Habasha 19 a kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:27+00:00 )
Jun 18, 2016 11:11 UTC
  • An gano gawawwakin 'yan gudun hijrar Habasha 19 a D/Congo

Magabatan Ma'aikatar 'yan gudun hijra ta kasar D/Congo ta sanar da gano gawawwakin 'yan gudun hijrar Habasha 19 a kasar

Wani Jami'i na Ma'aikatar 'yan gudun hijra a kasar D/Congo ya ce A yau Assabar Dakarun tsaron kasar sun gano gawawwakin 'Yan gudun hijra kasar Habasha 19 a cikin wata Mota da ta shigo kasar ta barauniyar hanya a yankin Katanga dake kudu maso gabashin kasar.

Jami'in ya ce a yayin da Jami'an tsaro suka dakatar da Motar 'yan gudun hijrar da ta shiga kasar ta barauniyar hanya suka fahimci cewa a kwai wani abu da ake kokarin boye wa, bayan kuma sun gudanar da bincike suka gano gawawwaki 19 da suka rasa rayukansu sakamakon cunkoson dake cikin motar.

Ma'aikatar ta sanar da cewa dukkanin mutanan da suke cikin motar da adadinsu ya kai 95 da kuma suka shigo kasar ta barauniyar hanya 'yan kasar Ethiopia ne, inda suke kokarin shiga kasar Afirka ta kudu daga nan kuma su fice zuwa kasar Kenya.

Rahoton ya ce a ko wata shekara duban 'yan kasar Ethiopia ne ke bi ta kasashen D/Congo da Afirka ta kudu inda suke isa zuwa kasar Kenya domin neman abinda za su korewa bakunan kuda.