'Yan Bindiga Sun Kashe Mutanen Kudu maso yammacin Najeriya 15
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6949-'yan_bindiga_sun_kashe_mutanen_kudu_maso_yammacin_najeriya_15
Najeriya: An Kashe mutane 15 A Jahar Ogun
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 19, 2016 14:41 UTC
  • 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutanen Kudu maso yammacin Najeriya 15

Najeriya: An Kashe mutane 15 A Jahar Ogun

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin ya nakalto cewa; Wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a yankin Ogijo da ke jahar Ogun, a kudu maso yammacin Najeriya inda su ka kashe mutane 15.

Tuni dai jami'an tsaro su ka fara gudanar da bincike domin gano maharan da kuma dalilinsa. Haka nan kuma majiyar 'yan sanda a yankin ta sanar da cewa abu ne mai yiyuwa a sami karuwar adadin wadanda su ka rasa rayukan nasu.

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.