Somaliya: Halakar Wani Jigo Na Kungiyar al-shabab
al-shabab ta Somaliya ta yi furuci da kashe wani jigonta.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato wani bayani da kungiyar al-shabab ta fitar a yau lahadi da a cikin take furuci da kashe Muhammad Muhammad Kuno wanda daya ne daga cikin kwamandojinta.
Bayanin ya ce an kashe Muhammad Muhammad Kuno ne a wani hari da jiragen yakin Amurka su ka kai a kasar.
Shi dai mutumin da aka kashe, wanda kuma ake dauka a matsayin daya daga cikin kusoshin kungiyar ta al-shabab, dan asalin kasar Kenya ne.
Bugu da kari, mutumin shi ne ya jagoranci wani harin ta'addanci da al-shabab ta kai a cikin Hotel din Embassador da ke birnin Magadishu, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Kungiyar ta al-shabab dai tana da alaka ne da kungiyar alka'eda, kuma tana fada da gwamnatin kasar Somaliya.