Murtaniya Ta soki Wani Kamfanin Kasar Canada Kan Hakar Gwal
Gwamnatin Murtaniya Ta Yi Tir da Tsaikon Da Aka Samu A Hako Zinariya da Wani Kamfanin Canada Ya ke yi.
Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) daga kasar Murtaniya ya ce; Gwamnatin kasar ta yi tir da matakin da wani kamfanin kasar Canada ya dauka na dakatar da hako zinariyar da ya ke yi a cikin kasar.
Kamfanin na kasar Canada mai suna Kinrass wanda ya kulla yarjejeniya da gwamnatin kasar ta Murtaniya akan hako zinairiyar, ya sanar da dakatar da ayyukansa ayau lahadi. Kamfanin dai ya ce; Dalilin dakatar da ayyukan nashi, shi ne tsoma bakin da ma'aikatar masana'antun kasar ta ke yi a cikin ayyukansa.
A cikin shekaru 6 na aikin kamfanin Canada a cikin kasar ta Murtaniya an sha samun sabani a tsakaninsa da ma'aiakata.
Wurin da ake hako zinariyar dai shi ne mafi girma a cikin kasar ta Murtaniya kuma kamfanin na kasar Canada ne ya ke tafiyar da shi.