Shugaba Buhari ya koma gida
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6970-shugaba_buhari_ya_koma_gida
Bayan jinyar ciwon kunne na kusan makwanni biyu a birnin London A jiya Lahadi Shugaban Najeriya Muhamad Buhari ya koma gida.
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 20, 2016 01:17 UTC
  • Shugaba Buhari ya koma gida

Bayan jinyar ciwon kunne na kusan makwanni biyu a birnin London A jiya Lahadi Shugaban Najeriya Muhamad Buhari ya koma gida.

Shugaban ya sauka ne a babban filin jirgin sama na birnin tarayya Abuja, da misalin karfe biyar na yammancin jiya Lahadi

Manyan jami'an gwamnati da dama ne suka tarbi shugaban a lokacin da ya sauka.

Ana kuma sa ran zai koma bakin aiki a wannan Litinin, domin cigaba da tafiyar da al'amuran kasar.

A ranar shida ga watan da muke ciki(06.06.2016), Shuagaba Buhari dan shekaru 73 da haifuwa yatafi birnin London domin yin jinyar ciwon kunnen da yake fama da shi , bisa shawarar da wasu likitoci suka bashi a Najeriya.

Tun da fari an shirya shugaba Buhari zai dawo ranar Alhamis da ta gabata ne, amma sai ya jinkirta dawowar tasa zuwa jiya Lahadi domin ya kara hutawa.

A ranar Alhamis din ne kuma mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo ya sanar da cewa Buhari ya samu lafiya kuma zai dawo ranar Lahadi.