Najeriya : Sabon Tsarin CBN Ya Nakasa Naira
-
darajar Naira ta fadi da kashi 23 cikin dari
Rahotanni daga Najeriya na cewa darajar kudin kasar wato Naira ya fadi da kashi 23% a ranar farko ta fara amfani da sabon tsarin musayar kudaden ketare, bayan da babban bankin kasar (CBN), ya janye kariyar da ya baiwa Nairar.
Bayanai daga kasar sun nuna cewa a yau Litinin anyi musayar Naira wajajen 250-255 a kan dala daya a kasuwannin hukuma, yayin da ta kai 325-345 a kan kowacce dala a kasuwannin bayan fage.
Faduwar farashin man fetur a duniya wanda kasar ta dogara dashi shi ne umal aba'isin durkushewar tattalin arzikin wannan kasa ta Najeriya, wace ake yiwa kallon mafi yawan tattalion arziki a Nahiyar Afrika.
Wannan matakin dai ya samu karbuwa sosai daga kwararu da dama wadanda ke ganin zai janyo masu zuwa jari da kasar ke matukar bukata a halin yanzu.
Masu zuba jari dai sun jima suna kira ga gwamnatin Najeriya data karya darajar Naira saboda yadda karancin kudin kasashen wajen yayiwa tattalin arzikin kasar illah, aman shugaban kasar Muhamadu Buhari ya ce irin wannan matakin zai ragargaza kudin kasar.