RCA : An yi Garkuwa Da 'Yan Sanda A Bangui
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i6997-rca_an_yi_garkuwa_da_'yan_sanda_a_bangui
Rahotanni daga jamhuriya Afrika ta tsakiya na cewa dariruwan mutane ne suka tsere daga Bangui bayan da dakarun kasar hadin gwiwa dana kasa da kasa suka yi diran mikiya a unguwar musulmi ta PK5 inda akayi garkuwa da 'yan sanda.
(last modified 2018-08-22T06:58:28+00:00 )
Jun 20, 2016 13:39 UTC
  • RCA : An yi Garkuwa Da 'Yan Sanda A Bangui

Rahotanni daga jamhuriya Afrika ta tsakiya na cewa dariruwan mutane ne suka tsere daga Bangui bayan da dakarun kasar hadin gwiwa dana kasa da kasa suka yi diran mikiya a unguwar musulmi ta PK5 inda akayi garkuwa da 'yan sanda.

Mutane uku ne suka rasa rayukan su a musayar wuta da akayi a cewar rahotanni.

hadin gwiwar dakarun sunyi dira mikiya a unguwar ne bayan da wasu tsageru sukayi kunnan uwar shegu akan kiran gwamnati na su saki 'yan sandan guda shida da suek garkuwa dasu.

Bayanai daga yankin sun ce harkokin zirga zirga a hanyoyi da dama sun tsaya ciki a wannan unguwa, a yayin da kuma wani jirgin sama mai saukar ungulu ke shawagi.