Sabon Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika Ya Jaddada Wajabcin Yaki Da Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i70-sabon_shugaban_kungiyar_tarayyar_afrika_ya_jaddada_wajabcin_yaki_da_ta'addanci
Sabon shugaban kungiyar tarayyar Afrika ya yi suka kan rashin daukan kwararan matakan da suka dace a fagen yaki da ta'addanci a kasashen nahiyar Afrika.
(last modified 2018-08-22T06:57:44+00:00 )
Feb 01, 2016 03:15 UTC
  • Sabon Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika Ya Jaddada Wajabcin Yaki Da Ta'addanci

Sabon shugaban kungiyar tarayyar Afrika ya yi suka kan rashin daukan kwararan matakan da suka dace a fagen yaki da ta'addanci a kasashen nahiyar Afrika.

A ganawarsa da manema labarai a gefen bayan taron kungiyar tarayyar Afrika a birnin Adis-Ababa na kasar Habasha a jiya Lahadi: Sabon shugaban kungiyar tarayyar Afrika kuma shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya bayyana cewa; Yana daga cikin manyan ayyukan da suke gaban kungiyar tarayyar Afrika kokarin ganin an karfafa matakan yaki da ta'addanci da nufin ganin an samu nasarar wanzar da zaman lafiya da sulhu a nahiyar.

Har ila yau sabon shugaban kungiyar ta tarayyar Afrika ya jaddada cewa; Dukkanin shugabannin kasashen tarayyar Afrika sun jaddada aniyarsu ta hada kai tare da aiki tare a fagen yaki da ta'addanci domin samun nasarar murkushe ayyukan ta'addanci da suke ci gaba da addabar nahiya.

A jiya Lahadi ce aka zabi shugaban kasar Chadi Idriss Deby a matsayin sabon shugaban kungiyar tarayyar Afrika a yayin zaman taron kungiyar karo na 26, kuma zaman shugabannin kungiyar ta AU ya fi mai da hankali ne kan neman hanyoyin bunkasa ci gaban nahiyar, kare hakkokin bil-Adama musamman mata da kuma neman hanyar murkushe ayyukan ta'addanci da suke ci gaba da addabar nahiyar.