Shugaba Buhari Ya Nada Sabon Shugaban Yan Sandan Nigeria
Jun 22, 2016 06:49 UTC
An nada sabon shugaban yansanda a tarayyar Nigeria
Shugaba Mohammad Buhari a tarayyar ya nada Ibrahim Idris Kpotun a matsayin shugaban yan sandan Nigeria. Majiyar Jaridar Sahara reporters ta bayyana cewa shugaban zai maye gurbin Solomon Arase da Ibrahim Idris wanda ya yi ritaya daga aikin yansanda a yau Laraba.
Ibrahim Idris dai shi ne mataimakin shugaban yan sanda na kasa ne sannan ya taba shugabantar yansanda na jihar Kano.
Majiyar ta kara da cewa shugaban yana ganawa da jami'an yansandan a lokacinda aka hada wannan rahoton.
Tags