Somaliya: Mummunan Hari A kusa da Babban Birnin Kasar
Mutane da Dama Sun Mutu Sanadiyyar Wani Mummunan Hari A Kusa Da Birnin Magadishu
Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua ya ambato shaidun ganin ido suna cewa; harin da aka kai a yankin Hodan a jiya laraba, ya kashe mutum guda da jikkata wasu shida.
Jami'in gwamnati a yankin Abdullatif Omar Halaneh wanda ya tabbatar da kai harin, ya ce ; an yi amfani da makaman roka-roka da marecen jiya laraba.
Wani dan jarida a yankin Umar Farah wanda ya ke aiki da Rediyo yana daga cikin wadanda su ka jikkata,kuma wata sarakuwarshi da su ke tare ta mutu.
Harin dai an kai shi ne kusa da wani asibitin soja, sai dai mafi yawancin wadanda su ka jikkatan kananan yara ne.
Kawo ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai ana zargin kungiyar al'shabab da hannu.