Turai za ta bunkasa alakar tsaro da kasashen Afirka Ta yamma.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7204-turai_za_ta_bunkasa_alakar_tsaro_da_kasashen_afirka_ta_yamma.
Turai Za ta bunkasa alaka da Afirka ta yamma domin fada da ta'addancin a yankin
(last modified 2018-08-22T06:58:29+00:00 )
Jun 25, 2016 02:40 UTC
  • Turai za ta bunkasa alakar tsaro da kasashen Afirka Ta yamma.

Turai Za ta bunkasa alaka da Afirka ta yamma domin fada da ta'addancin a yankin

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua, ya nakalto cewa a jiya juma'a ne aka kawo karshen taron da kwamitin tarayyar turai din na kulla yarjejeniya mai muhimmanci, wanda aka yi a Lome na kasar Togo.

Taron dai ya maida hankali ne akan yadda za a fuskanci barazanar ta'addanci.

Bugu da kari, kwamitin ya bayyana takaicinsa akan yadda ake kara kai hare-haren taddanci a yammacin Afirka, tare da cewa babu yadda za a yi yankin ya ci gaba idan babu tsaro.

Wasu daga cikin shawarwarin da kwamitin ya bijiro da su, sun kunshi ganin cewa an kafa 'yansanda na yammacin Afirka da kuma daukar kwararan matakai akan masu kamun kifi ba bisa ka'ida ba.