Angola: kira Da A Saki Fursunonin Siyasa
Jun 25, 2016 02:45 UTC
Amnesty International Ta Kirayi Gwamnatin Angola da ta Saki Fursunonin Siyasa.
Kungiyar Kare hakkin bil'adama ta Amnesty Internation, ta kira yi gwamnatin Kasar Angola da ta saki wasu mutane 17 masu fafutukar kare tsarin demokradiyya da ake tsare da su.
Mutanen dai an kame su ne da kuma tsare su saboda halartar wani taro akan tsarin demokradiyya a birnin Luanda.
Gwamnatin kasar ta zargi mutanen da cewa 'yan tawaye ne da su ke kitsa makarkashiya.
An gudanar da zanga-zanga a cikin birane da dama na kasar domin ganin an saki mutanen 17
Tags