Birnin Magadishou Na Kasar Somalia Ya Girga Sakamon Tashin Wasu bama-Bamai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7246-birnin_magadishou_na_kasar_somalia_ya_girga_sakamon_tashin_wasu_bama_bamai
Rahotanni daga kasar Somalia na cewa wasu bama-bamai masu karfin gaske sun tarwatse yau a cikin birnin, lamarin da ya girgiza sassa daban-daban na birnin.
(last modified 2018-08-22T06:58:30+00:00 )
Jun 25, 2016 11:38 UTC
  • Birnin Magadishou Na Kasar Somalia Ya Girga Sakamon Tashin Wasu bama-Bamai

Rahotanni daga kasar Somalia na cewa wasu bama-bamai masu karfin gaske sun tarwatse yau a cikin birnin, lamarin da ya girgiza sassa daban-daban na birnin.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto daga majiyoyin tsaro a birnin na Magadishou cewa, wasu mutane ne suka ajiye wata mota da suka shakare da bama-bamai kuma suka tayar da ita a kusa da wani Otel, kafin daga bisani kuma suka shiga cikin otel din suka bude wutar bindiga kan mai uwa da wabi, majiyoyin ba su karin haske kan adadin mutane da suka rasu ko jikkata ba, amma shedun gani da ido sun kimanin 15 sun mutu.

 

A farkon wannan wata na Yuni 'yan ta'addan kungiyar Takfiriyyah wahabiyyah ta Al-shabab sun kaddamar da wani hari makamancin wannan a kan katafaren otel na ambassador, inda suka kashe mutane 20 tare da jikkata wasu kimanin 60.

 

Har yanzu babu wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin harin na yau a birnin Magadishou, amma tuni jami'an tsaro suka suka dora alhakin hakan kan kungiyar ta Al-shabab.