Karuwar kai hari a Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7267-karuwar_kai_hari_a_somaliya
Majiyar Asibitin Somaliya ta sanar da karuwar tashin Bom gami da kai hare-haren ta'addanci A Birnin Magadushu fadar shugabancin kasar
(last modified 2018-08-22T11:28:30+00:00 )
Jun 26, 2016 12:05 UTC
  • Karuwar kai hari a Somaliya

Majiyar Asibitin Somaliya ta sanar da karuwar tashin Bom gami da kai hare-haren ta'addanci A Birnin Magadushu fadar shugabancin kasar

Rahoton ya ce A jiya Asabar wasu mahara , suka kai hari a wani otel da ke Mogadishu babban birnin kasar Somaliya inda suka hallaka mutane da dama.

Da farko dai maharan sun soma da jefa wasu ababe masu tarwatsewa, kafin daga bisani su buda wuta da bindigogi masu sarrafa kansu.

Wasu Mutane da ke kusa da otel din da ake kira Naasa Hablood, sun tabbatar da cewa har ya zuwa wajejen karfe biyar na yammancin jiya Assabar ana ta harbe-harbe cikin otel din. Sai dai ba su san abun da ke faruwa ba, domin a daidai lokacin da suke shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP wannan labari, suna boye ne a wani guri domin tsira da rayukansu.

Wasu majiyoyi da dama na ma'aikatar tsaron kasar sun tabbatar da wannan hari, Rahotannin farko sun sanar da Mutuwar Mutane 15 tare da jikkatar wasu 27 na daban.

Tuni dai kungiyar Ashabab ta dauki alhakin kai harin.