Yadda Ficewa Britania Daga Tarayyar Turai Zai Shafi Yan Nigeria Mazauna Kasar
Akall yan Nigeria kimani 29,000 zasu dawo gida bayan ficewar Britania daga tarayyar Turai.
Bayan ficewar kasar Britania daga tarayyar Turai sakamakon zaben raba gardama na ranar Alhamis da ta gabata, yan Nigeria mazauna kasar Britania da dama zasu fice daga kasar.
Jaridar The Guardian ta Nigeria ta nakalto masana suna fadar cewa yan Nigeria wadanda abin zai shafa sun hada da wadanda basa da cikakkun takardun zama kasar, wato bakin haure. Banda haka abin zai shafi wadanda suka auri turawa tare da amfani da Visar Iyali na tarayyar Turai, wadanda suke da Passport na tarayyar turai da kuma Ma'aikata.
Sai dai ma'aikata wadanda suka hada da likitoci da malaman makarantu ba zasu fuskanci wata matsala a zamansu a Britania ba, inji rahoton.
Wata majiya ta bayyana cewa a karshen shekara ta 2011 kididdiga ya nuna cewa akwai yan Nigeria 210,184 da suke zaune a kasar Britania. Banda haka akwai yara yan kasa da shekara 18 wadanda suke da iyaye yan Nigeria amma basa daukar kansu a matsayin yan Nigeria, yawansu ya ninka wannan adadin. A halin yanzu dai akwai yan Nigeria kimani 29,000 wadanda za'a dawo da su gida.