Fasa Gidan Yari A Abuja :Charles Okah Yana Hannu Haryanzu
Hukumar kula da gidajen yara a Nigeria ta ce har yanzun Charles Okah yana tsare a gidan yari na Kuje a Abuja.
Har yanzun Charles Okah dan uwan Henry Okah shugaban kungiyar tsagerun Niger Dalter (MEND) yana tsare A Abuja bayan fasa gidan yarin da aka yi.
Jaridar Sahara reporters ta yanar gizo ta nakato Farncis Enobore kakakin hukumar kula da gidajen yara na kasa yan afadar haka a Abuja. Kafin haka dai an bada labarin cewa Okah yana daga cikin fursinonin da suke tsere a lokacinda aka fasa gidan yarin Kuje a birnin Abuja a jiya da dare.
Majiyar ta hukumar ta kara da cewa mutanen da suka guda a jiya da dare sune Maxwell Ojukwu daga jihar Delta da kuma Solomon Amodu daga jihar Kogi, kuma a halin yanzu jami'an tsaro suna kokarin kamasu don dawo da su gidan kaso.
Ana zargin Charles Okah da hannu a hare haren bom na ranar samun 'yencin kan Nigeria a Abuja, kuma tuni dan uwansa kuma shugaban kungiyar yan ta'adda ta (MEND) Henry Okah yana cin kaso na shekaru 24 a kasar Afrika ta Kudu.