Somaliya : Harin Al'shabab Ya Rutsa Da Sakataren Gwamnati
Ma'aikatar harkokin wajen Somaliya ta sanar da mutuwar sakataren gwamnatin kasar na muhalli, a harin da tsagerun Al'shabab suka kai a katafaren otel din nan dake Mogadisho babban birnin kasar.
Harin na Jiya Asabar wanda kungiyar ta Al'shabab ta dauki alhakin kaiwa yayi sanadin mutuwar mutane 11 a cewar ma'aikatar tsaro kasar ta Somaliya.
Gwamnatin ta Somaliya tayi amfani da wannan damar domin isar da ta'aziyar ta ga iyalan jami'in mai suna Buri Mohamed Hamza wanda aka gano gawarsa yau Lahadi a cikin wandanda harin Otel din na ''Naasa Hablood ''ya rusa dasu.
An dai kai harin ne da mota wanda yayi ragargaza wani bangaren otel, kafin daga bisani wani dan bindiga ya kusa kai a cikin ginin ya kuma buda wuta na kan mai uwa dawabi kan jama'a dake a ciki.
kungiyar Al'shabab dai ta kai hare-hare da dama makamantan wadanan a cikin wannan wata a otel-otel da dama a kasar ta Somaliya.