An Kai harin kunar bakin wake a Masalaci na garin Maiduguri
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7318-an_kai_harin_kunar_bakin_wake_a_masalaci_na_garin_maiduguri
Wasu 'Yan kunar Bakin wake da ake kautata zaton 'yan Boko haram ne sun kai hari a wani Masallaci na garin Maiduguri
(last modified 2018-08-22T06:58:30+00:00 )
Jun 27, 2016 06:00 UTC
  • An Kai harin kunar bakin wake a Masalaci na garin Maiduguri

Wasu 'Yan kunar Bakin wake da ake kautata zaton 'yan Boko haram ne sun kai hari a wani Masallaci na garin Maiduguri

A Najeriya, wasu 'yan kunar-bakin-wake da ake zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun rasa ransu bayan da bama-bamai suka tashi da su a lokacin da suke kokarin shiga wani masallaci daren jiya lahadi a birnin Maiduguri da ke jihar Borno.

Rahotanni na cewa maharan dai sun je masallacin ne da nufin shiga sahun Sallah a lokacin da jama'a suke tsaka da Sallar dare da aka fi sani da Kiyamullaili, a wani masallaci da ke Damboa Road.

Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewa 'yan kunar-bakin-waken ne kawai suka hallaka.

Yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a kusan dukkanin masallatan da ke birnin na Maiduguri.

A bangare guda, Majiyar tsaron Sojin kasar ta sanar da ceto Mazauna kauyukan arewa maso gabashin kasar 6 da adadinsu ya kai dubu biyar tare kuma da tsarkake su daga mayakan boko haram.