Barkewar Sabon Rikicin Siyasa A Kasar Madagascar:
Sabani Tsakani Gwamnati Da 'Yan hamayya A Madagascar.
Kamfanin Dillancin Labarun Faransa daga birnin Antananarivo ya ambato cewa; sabon rikicin siyasar da ya kunno kai a cikin kasar ya fi na baya tsanani.
A jiya lahadi ne dai wani bom ya tashi a wurin wasa na Mahamasina da ke babban birnin kasar, a daidai lokacin da ake wani biki na kasa. Mutane biyu ne dai su ka mutu yayin da wasu 82 su ka jikkata.
Wani dan hamayyar siyasa Guy Rivo Randroanarisoa ya bayyana cewa; Abu ne mai sauki gwamnatin kasar ta zargi 'yan hamayya da jawo hargitsi a cikin kasar.
Shi ma tsohon pira minitsan kasar Omer Beriziky, ya ce; abu ne mai yiyuwa sabanin da ake da shi ya kai ga daukar tsauraran matakai.
A cikin watannin bayan nan dai kasar ta fada cikin rikicin siyasa wanda ya sa 'yan hamayya suka yi kira da a gudanar da zaben gaggawa.
Shugaban Kasa Rajaonarimampisaniya ya shiga cikin shekara ta uku ta mulkinsa sai dai har yanzu babu alamar warware matsalar tattalin arzikin kasar.