Afirka ta Tsakiya : An Kashe Wani Sojan MDD
An Kashe Wani Sojan Majalisar Dinkin Duniya A Kasar Afirka ta Tsakiya
Jaridar Faransa ta Lo Figaro, ta ambato cewa; a yau litinin ne wani sojan tabbatar da zaman lafiya da ke karkashin rundunar majalisar dinkin duniya ta Minoska, ya mutu sanadin harin da masu dauke da makamai su ka kai a birnin Bongui.
Majiyar majalisar dinkin duniyar a kasar ta Afirka ta tsakiya ta ce; Sojan da aka kashe dan asalin kasar Senegal ne, kuma tuni an bude bincike akai.
Wannan dai ba shi ne karon farko ba da aka kai wa sojojin majalisar dinkin duniyar hari, acikin kasar ta Afirka ta tsakiya da sauran kasashe.
Manzon Musamman na babban magatakardar majalisar dinkin duniya a cikin kasar, ya ce; harin akan dakarun zaman lafiyar, laifin yaki ne.
Tun a 2014 ne majalisar dinkin duniya ta aike da sojojin tabbatar da zaman lafiya zuwa kasar ta Afirka ta tsakiya wacce ta yi fama da rikice-rikice.