Afrika Ta Kudu : Dole Zuma Ya Biya $ 500,000
Ma'aikatar kudi a Afrika ta kudu ta umurci shugaban kasar Jacob daya biya $ 500,000 a matsayin wani bangare na kudaden da yayi amfani dasu wajen gyaran gidansa.
Kotu Afrika ta Kudu ce ta nemi ma'aikatar baitalmalun kasar data hakikance yawan kudaden gwamnati da Mr Zuma ya yi amfani dasu wajen gyaran gidansa.
Kudaden da Mr Zuma zai biya na zamen kashi daya ne cikin ayukan da aka gudanar a gidan sa a cewar wata wasika da ma'aikatar kudi ta kasar ta aikewa kotun tsarin mulkin kasar.
An dai jima ana kace-nace kan wannan badakala ta ayyukan fadada gidan Mr Zuma, inda a karshen watan Maris kotun tsarin mulkin kasar ta ce Zuma ya take kundin tsarin mulki saboda kin amunce biyan kudaden gyaran gidan nasa wanda ba bangaren tsaro ba, hasali ma sun shafi abubuwan jin dadin rayiwasa ne, lamarin daya sa 'yan adawan kasar shigar da kara Zuma kan amfani da kudaden gwamnati.
Yanzu dai kotun tsarin mulkin kasar ita ce keda maganar karshe akan kudaden da aka kayyade, sanan idan ta amunce Zuma nada kwana 45 domin biyan kudaden.