Kame Wani Dan tawayen Kasar Uganda A Kasar Afirka ta tsakiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7396-kame_wani_dan_tawayen_kasar_uganda_a_kasar_afirka_ta_tsakiya
Majiyar Tsaron Afirka ta tsakiya ta sanar da kame wani kwamandan kungiyar 'yan tawayen Uganda.
(last modified 2018-08-22T06:58:31+00:00 )
Jun 29, 2016 04:02 UTC
  • Kame Wani Dan tawayen Kasar Uganda A Kasar Afirka ta tsakiya

Majiyar Tsaron Afirka ta tsakiya ta sanar da kame wani kwamandan kungiyar 'yan tawayen Uganda.

Tashar taelbijin din France Info ta bada labarin cewa; Jami'an tsaron kasar Afirka ta tsakiya tare da hadin guiwar rundunar sa-kai, sun yi nasarar gano mabuyar kwamandan 'yan tawayen kasar Uganda, tare kuma da kame shi.

Rundunar sa-kai din wacce aka fi sani da Rundunar al'umma domin gina sabuwar Afirka ta tsakiya, ce dai ta fara bada labarin kama kwamandan kungiyar ta " Lord Resistance Army"

Kawo ya zuwa yanzu dai babu wani karin bayani daga majiyar tsaron akan sunan, kwamadan da aka kama.

Sai dai sanarwar ta zo ne bayan wasu jerin hare-hare da kungiyar 'yan tawayen Ugandan ta kai a garuruwan Zimyo da Bakoma da Bangaso da su ke a gabacin kasar ta Afirka ta tsakiya. Hare-haren dai sun kashe mutane da dama.

Kungiyar Lord Resisitance Army dai an kafa ne tun a 1987 a kasar Uganda da zummar kifar da gwamantin shugaba Uweri Musaveni. Kuma ta shahara da daukar kananan yara a matsayin soja, da kuma azabtar da mutane ta hanyar yanke musu kafafufuwa ko hannaye.