Mutane 18 ne suka rasu sanadiyar tashin Nakiya a kudancin Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7456-mutane_18_ne_suka_rasu_sanadiyar_tashin_nakiya_a_kudancin_somaliya
Tashin Nakiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18 a kudancin kasar Somaliya
(last modified 2018-08-22T06:58:31+00:00 )
Jun 30, 2016 06:45 UTC
  • Mutane 18 ne suka rasu sanadiyar tashin Nakiya a kudancin Somaliya

Tashin Nakiya ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18 a kudancin kasar Somaliya

Jami'an 'yan sandar Somaliya sun sanar a wannan Alkhamis cewa akalla fasinjoji na wata karamar Bas 18 ne suka rasa rayukansu sanadiyar tashin wata Nakiya a kusa da hanyar garin Lafole dake kudu maso yammacin Magadushu fadar milkin kasar Somaliya, kuma dukkanin wadanda suka rasun fararen hula ne.

Rahoton ya ce karamar Bas din na bin wata babbar Motar Jami'an tsaro ne a yayin da nakiyar ta tashi da ita.

Ganau da ido sun ce an kai harin ne da nufin tayar da babbar motar jami'an tsaron, sai harin ya ritsa da motar fararen hular. kuma ita motar Jami'an tsaron babu abinda ya same ta.

Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai wasu na ganin cewa kungiyar Ashabab ce ta kai shi.