Sudan : MDD Ta Tsawaita Aikin Tawagar Ta A Darfur
Kwamitin sulhu na MDD ya kara wa'adin aikin tawagarsa da kuma na tarayya Afrika a yankin Darfur na Sudan da shekara guda.
MDD ta amuncxe da wannan kudiri ne a Jiya Laraba duk da adawar da mahukuntan Khartum suke da hakan.
Babban sakatare na MDD ne Ban-ki-Moon da shugabar kungiyar tarayya Afrika ta (AU) ne Nkosazana Dlamini-Zuma suka bukaci tsawaita aikin tawagar.
kwamitin ya ce yanayin da ake ciki a yankin na Darfur dake yammacin Sudan babbar barazana ne ga zamen lafiya na kasar dama tsaron kasa da kasa.
Kimanin dakaru da 'yan sanda 18.000 ne na tawagar ta MINUAD ke jibge a yankin na Darfur inda dubban fararen hula suka rasa rayukan sanadin rikicin da yaki ci yaki cinyewa tun farkon sa shekara 2003.
Al'kalumen da MDD sun nuna cewa rikin yankin yayi sanadin mutuwar mutane 300.000 tare da cilastawa wasu kimanin miliyan 2,5 kauracewa muhalensu.