Ranar Qudus
Ranar Qudus Ta Duniya A Najeriya
A Najeriya an gudanar da Zanga-zangar ta lumana a cikin biranen katsina da Potuskum, yayin da ake shirin gudanar da iya idan an idar da sallar juma'a a birnin kano.
Masu Zanga-zangar a birnin katsina sun daga kwalye da kyallaye dauke da taken yin tir da zaluntar al'ummar Palasdinu da 'yan sahayoniya su ke yi.
A garin Potuskum da ke Jahar Yobe ma an sami dandazon masu zanga-zangar da su ka fito daga cikin birnin da kuma garuruwan da su ke kusa.
A kowace shekara dai harkar musulunci a karkashin Sheik Ibrahim Yakub al-zakzaky tana gudanar da zanga-zangar ranar qudus ta duniya daidai a ranar juma'ar karshe ta watan Ramadhan bisa amsa kiran jagoran juyin musulmi, Marigayi Imam Khumain. (r.)