Zanga-zangar Raya Ranar Qudus A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7510-zanga_zangar_raya_ranar_qudus_a_najeriya
Duk da cewa Jagoran 'yan uwa a Najeriya musulmi na tsare, duban magoya bayan sa sun gudanar da zanga-zangar raya Ranar Qudus a Jahohi daban daban na kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:31+00:00 )
Jul 01, 2016 13:43 UTC
  • Zanga-zangar Raya Ranar Qudus A Najeriya

Duk da cewa Jagoran 'yan uwa a Najeriya musulmi na tsare, duban magoya bayan sa sun gudanar da zanga-zangar raya Ranar Qudus a Jahohi daban daban na kasar

Jaridar Daily Trust ta habarta cewa Al'ummar musulmi Almajiran shekh Ibarahim Yakoubu Al-zakzaky sun gudanar da zanga-zangar raya ranar Qudus a jahohi daban daban na cikin kasar duk kuwa da cewa Jagoran su da wasu mukarabansa na tsare a hanun hukuma.

Mahalarta Zanga-zangar a birnin katsina sun daga kwalye da kyallaye dauke da taken yin tir da zaluntar al'ummar Palasdinu da 'yan sahayoniya su ke yi.

A garin Potuskum da ke Jahar Yobe ma an sami dandazon masu zanga-zangar da su ka fito daga cikin birnin da kuma garuruwan da su ke kusa.

A Garin Kanon Dabo ma duban magoya bayan shekh Ibrahim Zakzaky ne suka gudanar da zanga-zangar bayan kamala sallar Juma'a

A kowace shekara dai harkar musulunci a karkashin Sheik Ibrahim Yakub al-zakzaky tana gudanar da zanga-zangar ranar qudus ta duniya daidai a ranar juma'ar karshe ta watan Ramadhan bisa amsa kiran jagoran juyin musulmi, Marigayi Imam Khumain.

A shekarar 2014, Dakarun tsaron Najeriya sun kai farmki kan mahalarta zanga-zangar Qudus din a garin Zariya, inda suka kashe Mutane 33 daga cikin su a kwai 'ya'yan shekh Ibrahim Azakzaky guda uku.