Shirin kara hanun jarin bangaren Iskar Gaz A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7516-shirin_kara_hanun_jarin_bangaren_iskar_gaz_a_najeriya
Shugaban hukumar dake kula da harakar iskar Gaz a Najeriya ya sanar da cewa a kwai damar kara saka hanun jari na sama da $ biliya 55 da kuma hakan na iya kasance riba a nan gaba.
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 01, 2016 13:45 UTC
  • Shirin kara hanun jarin bangaren Iskar Gaz A Najeriya

Shugaban hukumar dake kula da harakar iskar Gaz a Najeriya ya sanar da cewa a kwai damar kara saka hanun jari na sama da $ biliya 55 da kuma hakan na iya kasance riba a nan gaba.

Mista Bolaji Asansania ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da manya 'yan kasuwa masu zuba hanun Jari a taron shekara shekara shekara da ya gudana a birnin Legas, inda ya kara da cewa matukar 'yan kasuwar suka zuba jarin su a wannan bangare domin gano da kuma tace iskar Gaz din, cikin kankanan lokaci za su iya mayar da kudaden su kuma su samu kazamar riba.

Mista Bolaji ya ce ci gaba da fitar da iskar Gaz a kasar na bukatar babban jari da hakan shi zai snya a kara samar da Iskar Gaz din a kasar ya wadatu har ma a ci gaba da sayar da shi a kasashen ketare.

Shugaban Ya ce Gwamnatin Tarayya da kuma masu sanya hanun Jarin sun gano cewa a matakin farko a samar da wata doka wacce za ta kore duk wani kokonto tsakanin bangarorin biyu, domin tabbatuwar hakan, Hukumar sa za ta zauna tare da kwamitin Majalisar Dattijai a karshen wannan shekara.