Tsaurara Matakan Tsaro A Yankin Kanyama Na Jamhuriyar DR Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7531-tsaurara_matakan_tsaro_a_yankin_kanyama_na_jamhuriyar_dr_congo
Kantomar yankin Kanyama da ke lardin Haut-Lomami a kudancin Jamhguriyar Dimokaradiyyar Congo ya sanar da cewa; Jami'an tsaron yankin sun tsaurara matakan tsaro da nufin dakile hare-haren wuce gona da iri.
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 02, 2016 01:01 UTC
  • Tsaurara Matakan Tsaro A Yankin Kanyama Na Jamhuriyar DR Congo

Kantomar yankin Kanyama da ke lardin Haut-Lomami a kudancin Jamhguriyar Dimokaradiyyar Congo ya sanar da cewa; Jami'an tsaron yankin sun tsaurara matakan tsaro da nufin dakile hare-haren wuce gona da iri.

Kantomar yankin Kanyama da ke lardin Haut-Lomami a Kudancin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Laurent Kiyoko Lukemba ya sanar da cewa: Jami'an tsaro a yankin suna cikin shirin ko ta kwana da nufin kalubalantar duk wani harin wuce gona da iri da yankin ke fuskanta daga wasu gungun 'yan bindiga da ake kyautata zaton barayi ne.

Laurent ya kara da cewa; gwamnati ta wadata Jami'an tsaron da suka hada da sojoji da 'yan sanda da makamai da na'urorin sadarwa domin kawo karshen kai hare haren wuce gona da iri a yankin.

A makon da ya gabata ne wasu gungun 'yan bindiga suka farma yankin da muggan makamai tare da wawushe dukiyoyin jama'a.