Najeriya: Kashe Ma'aikatan Mai 3 'yan Kasar Waje
"Yan fashin Doron Ruwa Sun Kashe 'Yan Kasar Italiya 3.
Kamfanin Dllancin Labarun Faransa ya ambato cewa; wasu mutane dauke da makamai sun kai hari a kudancin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar Italiyawa 3 da su ke aiki da kamfanin Agip.
Wani jami'in tsaro a yankin da lamarin ya faru, a jahar Bayelsa, Dozmond Ego, ya ce; wasu mahara ne su kai harin inda su ka shammaci ma'aikatan kamfanin (AGIP) su 3 a lokacin da su ke gyaran bututun mai.
Dozmand ya kuma tabbatar da gano gawawwakin mutane biyu na wadanda aka kashe din a cikin ruwa.
Wata majiyar ta ce; mutane biyun, injiniyoyi ne sai kuma direban kamfanin Agip.
Harkokin tsaro dai a wannan yankin, sun dagule.
A wani labarin kuma, Mai magana da yawun 'yan sanda Moses Yamu ya ce; An sace wasu 'yan asalin kasar Indiya biyu a kan hanyarsu ta zuwa Gboko babban birnin jahar Benue.
H