Sudan Ta Yi Fatali Da Rahoton Amurka Game Da Safarar Mutane
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i7618-sudan_ta_yi_fatali_da_rahoton_amurka_game_da_safarar_mutane
Gwamnatin Sudan ta musanta rahoton Amurka wanda ya ambata kasar a matsayin daya daga cikin kasashen duniya da sa tanaka komai game da yaki da safarar bil adama.
(last modified 2018-08-22T06:58:32+00:00 )
Jul 04, 2016 02:12 UTC
  • Sudan Ta Yi Fatali Da Rahoton Amurka Game Da Safarar Mutane

Gwamnatin Sudan ta musanta rahoton Amurka wanda ya ambata kasar a matsayin daya daga cikin kasashen duniya da sa tanaka komai game da yaki da safarar bil adama.

wata sanarwa da ma'aikatar sudan ta fitar ta ce rahoto ne marar hujja da rashin adalci.

Dama dai Amurkar ta saba wallafa rahoton game da safarar dan adam a duk shekara, inda a bana ta zayyana kasashen Syria da Sudan da wasu kasashen Larabawa hudu a matsayin wadanda basa tabaka komai game safarar bil adama.

Cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta fitar ta nuna cewar, dangane da Sudan rahoton na Amurka ba shi da tushe, kana abin da rahoton ya yi shi ne yunkurin zubarwa kasar mutunci a idanun duniya, baya ga irin nasarorin da kasar ta cimma musamman wajen hana tilasta yara kanana shiga aikin soji da safarar mutane.